Ku San Malamanku tare da Gwani Lawi Gwani Saleh Ɗanzarga

Ku San Malamanku tare da Gwani Lawi Gwani Saleh Ɗanzarga
An wallafa

Filin Ku San Malamanku a wannan makon ya tattauna da Gwani Lawi Gwani Saleh Ɗanzarga da ke birnin Kano a Arewacin Najeriya.

An haife shi a Daurawa da ke Ƙoƙi a jihar Kano kuma ya soma karatunsa ne a gaban mahaifinsa Gwani Salihu Ɗanzarga. Sai dai daga baya mahaifin nasa ya samo wani malami da yake karantar da su.

Ya ce ya zama gwani ne a shekarar 1979, kuma ya samu takardar shaidar kammala makarantar sakandare ta SAS da ke Kano.

Gwani Lawi ya ce babban burinsa shi ne ya samu kuɗi da zai kafa tsangaya, a yi tsarin da almajirai ba za su sha wahala ba.

Malamin ya ce yana da ƴaƴa shida da jikoki 15.