Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Sani Shuaib
Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Sani Shuaib
An wallafa
Filin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Sheikh Muhammad Sani Shuaib, malami a jihar Kano wanda aka haifa ranar 31 ga watan Disamban shekarar 1939.
Ya yi karatu a wajen Mallam Abubakar - mahaifin Mallam Nasidi Abubakar Goron Dutse.
Ya kuma ce a hannunsa ya yi karatun farko na Al-Qur'ani duk da cewa bai dade a wajensa yana karatu ba.
Ya kuma ce ya yi karatu a wajen Malam Inuwa Limamin Zawiya.




