Dalilan neman kirkiro hukumar hukunta laifukan zaɓe a Najeriya

An wallafa

Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudirin dokar kirkiro hukuma ta musamman da ta za ta rika daukar dawaniyar hukunta masu laifukan zabe.

A wani zama da ta yi a ranar Alhamis majalisar ta karbi rahoton kwamitinta na harkokin zaɓe kan wannan kuduri.

Yanzu za a gabatar da kudirin ga majalisar dattawa kafin ya je gaban shugaban kasa domin ya zama doka.

Shugabar kwamitin kula da harkokin zaɓe a majalisar wakilan Najeriya Hon. Aishatu Dukku ta shaida wa BBC cewa kafa wannan hukuma a yanzu na da matukar muhimmanci ganin irin laifukan da ake tafkawa kafin zaɓe da lokacin zaɓen da kuma bayan zaɓe.

‘Yar majalisar ta ce duk da cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka soma bijiro da wannan batu ba, sai dai a wannan lokaci ya zama wajibi a yi azama domin kauce wa kura-kuran baya.

Abin da kudirin ya kunsa

A cewar Aishatu Dukku, daftarin dokar ya nemi kafa hukuma ta musamman mai zaman-kanta da aikinta shi ne bibiyar laifukan zaɓe da sa ido domin tabbatar da cewa an yi wa kowa adalci.

Ta ce sanin kowa ne cewa galibin irin wadannan laifuka kalubale ne ga dimokuradiya.

Musamman a kasashe irin Najeriya, kuma tun kafin wannan gwamnati da ma ake maganar kirkiro wannan hukuma domin inganta dimokuradiyar.

Ta ce ayyuka na yi wa kotuna yawa don hakan a cikin laifuka dubbai da ake gabatar musu ba sa iya sauraron ko da kashi guda cikin hudu.

Wannan a ganin Aishatu Dukku na haifar da jinkirin shari'o'i da kuma bin hakkin masu korafi.

Amma da wannan hukuma komai zai zo cikin sauki, in ji ta.

Sannan ta ce kirkirar irin wannan hukuma ce kawai mafita, domin idan babu ita 'yan Najeriya ba za su fahimci cewa laifi ne, mutum ya tada fitina kafin zaɓe ko bayan zaɓe ko kuma a ranakun zaɓe ba.

'Matasa a bangar siyasa'

'Yar majalisar ta yi tsokaci kan batun amfani da yara ko matasa a wajen taron siyasa ko tunzura su, su tada tarzoma, ta ce duk laifuka ne da ke bukatar a duba su da hukunta masu hannu a ciki.

Ta ce irin wadannan abubuwan da ake kawar da kai su ke haifar da koma-baya ga ci-gaban dimokuradiya a Najeriya, don haka dole a tashi tsaye idan an shirya ganin sauyi.

Ta ce ba za a ɗau lokaci ba wannan hukuma za ta kafu, domin a matakin da suke sun tsallake matakin jin ra'ayoyin jama'a da kuma matsayar majalisar wakilai.

Karin haske

Tuni dai hukumar zabe, INEC, ta sakar wa jam'iyyun siyasa da 'yan takarar linzami domin fara yakin neman zabe, wanda galibin 'yan kasa ke fatan ganin an yi gangami a cikin tsafta.

Wannan dalili ne ya sanya aka cimma wata yarjejeniya da za ta tabbatar da zaman lafiya kafin lokaci da kuma bayan zaben. 

Babu kuma mamaki idan wannan hukuma ta tabbata, a ga sauyi wajen bin kadi da hakkokin masu korafi a lokacin da bayan zaɓe.