Yadda wata guguwa ta lalata wutar lantarki a Amurka

Yadda wata guguwa ta lalata wutar lantarki a Amurka
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wata gagarumar guguwar hamada ta yi ɓarna sosai a jihar Arizona ta Amurka.

Iska mai ƙarfi da ƙura da guguwa sun yi ta kaɗawa tun daga ranar Litinin.

An rufe hanyoyi tare da katse wutar lantarki a gidajen mutane a babban birnin jihar, Phoenix.

Ana samun ƙaruwar guguwa a jihar saboda shekarun da aka shafe ana fama da rashin ruwan sama da ayyukan haƙar ma'adinai waɗanda suka sa manoma rasa na yi saboda yadda gonakinsu ke komawa hamada.