Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG za ta yi wa Utd kancal kan Hojlund, Bayern na jiran Fabinho
Atalanta ba ta da niyyar sassautowa a kan farashin fam miliyan 86 da ta sanya wa dan wasanta na gaba na Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 20, wanda Manchester United ke matukar so.(Mail)
Ita ma Paris St-Germain na sha'awar Hojlund kuma tuni ma har ta fara tattaunawa a kansa. (L'Equipe)
Zakarun Jamus Bayern Munich na sha'awar dan wasan tsakiya na Liverpool Fabinho, na Brazil idan tafiyarsa Al-Ittihad ta Saudiyya ba ta tabbata ba. (Sky Germany )
Haka kuma Bayern din na shirin gabatar da tayi na uku a kan Harry Kane kuma kungiyar tana da kwarin gwiwar samun dan wasan na Tottenham. (Times)
Fiorentina ta ce har yanzu ba ta ji wata bukata a hukumance ba daga Manchester United a kan dan wasanta na tsakiya Sofyan Amrabat, na Moroko mai shekara 26. (Metro)
Dan bayan Ingila Kyle Walker, na son tattaunawa da Bayern Munich, yayin da yake shirin barin Manchester City a bazaran nan. (Sky Sports)
Crystal Palace na da kwarin gwiwa cewa Wilfred Zaha na Ivory Coast zai kulla sabuwar yarjejeniya da ita duk da goron gayyata da ya samu daga Al-Ettifaq da Lazio.(Telegraph)
Manchester City ta matsa domin samun amsar Bernardo Silva, kan tayin ba shi fam dubu 300 a duk mako idan ya yarda ya ci gaba da zama. (Mirror)
Nottingham Forest na kokarin samun 'yan wasa biyu daga Manchester United - dan wasan gaba na gefe na Sweden Anthony Elanga, wanda take son sayensa dindindin da kuma golan Ingila Dean Henderson, wanda take so aro. (Fabrizio Romano)
Atletico Madrid na shirin gogayya da Chelsea a kan dan gaban Montpellier Elye Wahi, dan Faransa mai shekara 20. (Express)
Sai dai Wahin ya ce ba ya son ya je aro kungiyar Starsbourg, wadda masu Chelsea ne suke da ita, idan har Chelsea ta saye shi. (Foot Mercato)
Alex Telles, na dab da kammala tafiyarsa kungiyar Al-Nassr daga Manchester United a kan fam miliyan 4.(Mirror)
Nottingham Forest ta kusa kammala daukar Ola Aina bayan kwantiragin dan bayan na Najeriya ya kare a Torino.(Nottingham Post)
Matashin dan bayan Southampton na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Tino Livramento, na dab da kammala shirin tafiyarsa Newcastle. (Chronicle Live)
Liverpool da Paris St-Germain da Atletico Madrid na sha'awar dan wasan tsakiya na Mali Cheick Doucoure, mai shekara 23, amma kuma kungiyarsa Crystal Palace tana bukatar sai an saye shi fam mliyan 65. (90 min)
Liverpool na tattaunawa da kungiyar Preston North End domin sayen matashin dan gabanta Layton Stewart, dan Ingila mai shekara 20. (Liverpool Echo)
Thiago, na duba yuwuwar barin Liverpool inda yake da zabin tafiya Sifaniya ko Saudiyya ko kuma Turkiyya. (Diario Sport)
Matashin dan bayan Holland Ki-Jana Hoever, mai shekara 21, da dan wasan gaba na gefe na Portugal Chiquinho, mai shekara 23, suna dab da tafiya Stoke aro daga Wolves. (Express da Star)
Dan bayan Fiorentina dan Brazil Igor, na dab da kammala gwajin lafiyarsa a Brighton ranar Litinin bayan da kungiyarsa ta amince ta sayar da shi a kan fam miliyan 14.7 (Fabrizio Romano)
Southampton ta yi watsi da tayi na biyu da Monaco ke yi wa dan bayanta na Ghana Mohammed Salisu, mai shekara 24, kuma watakila sai dai ta jira har zuwa watan Janairu lokacin kwantiraginsa ya kare ta dauke shi kyauta. (Mail)