Klopp zai sayo Aguerd Real Madrid na son daukar Davies

An wallafa

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp na son sayen ɗan wasan bayan West Ham ɗan ƙasar Morocco, Nayef Aguerd a bazara mai zuwa, ko da yake, zai iya fuskantar ƙalubale daga Manchester City, wadda ita ma ke son ɗan wasan mai shekara 27. (Sun)

Tsohon kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya yi watsi da tayin zama mai horas da ƙungiyar ƙwallo ƙafa ta matan Norway. (Mirror)

Real Madrid za ta yi ƙoƙarin sayen ɗan ƙwallon bayan Bayern Munich, mai shekara 22, Alphonso Davies a kakar baɗi. (Marca)

Chelsea da Barcelona da kuma Bayern Munich duk sun yi ƙoƙarin ɗaukar Marco Verratti, mai shekara 30, daga Paris Saint-Germain a kakar nan. (Football Transfers)

Sai dai ɗan wasan tsakiyar na ƙasar Italiya a yanzu ya mayar da hankalin tafiya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Qatar, Al Arabi daga PSG a kan yuro miliyan 45. (Fabrizio Romano)

Kocin Manchester United Erik ten Hag zai tattauna da Jadon Sancho a Litinin ɗin nan a karon farko tun da manajan ya zargi ɗan wasan gefen na Ingila da cewa ba ya ƙoƙarin da ya cancanci samun wuri a jerin ‘yan wasan ƙungiyar na farko. (Telegraph)

Tottenham na daf da ɗaukar ɗan ƙwallon baya na ƙasar Croatia, daga kulob ɗin Hajduk Split, Luka Vuskovic, wanda ake alakanta shi da Liverpool ko Chelsea ko PSG ko kuma Manchester City, sai dai matashin ɗan ƙwallon mai shekara16 ba zai koma ɗin Tottenham ba sai a 2025. (Standard)

Kocin Barcelona, Xavi ya shirya rattaba hannu a kan sabuwar kwanturagi da ƙungiyar ta Camp Nou a wannan mako. (Fabrizio Romano)

Aston Villa na ɗokin sayen ɗan wasa mai jefa ƙwallon ƙasar Sifaniya, Alex Baena, kuma matashi ɗan shekara 22, daga tsohuwar ƙungiyar koci Unai Emery, wato Villarreal. (Fichajes)

Inter Milan ta ƙi sallama tayin da Chelsea da Liverpool da kuma Newcastle United suka yi wa ɗan ƙwallonta na ƙasar Italiya, Nicolo Barella a kakar nan, sai dai za a iya sayen ɗan wasan a kan kimanin fam miliyan 77 a baɗi. (CaughtOffside)