An haifi dubban yara a Katsina bayan 'yan fashi sun yi wa mata fyaɗe
Shirin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna game da hare-haren 'yan fashin daji a Jihar Katsina.
A daidai lokacin da hare-haren ‘yan fashin suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a wasu jihohin arewacin Najeriya ciki har da Katsina, a yanzu haka wasu dattawa a jihar ta Katsina sun bullo da wani tsari domin aiki tare da jami’an tsaro ta yadda za su samar wa al’ummar jihar sauƙi.
Daga cikin dabarun da suka bullo da su har da daukar matasa 100 a kowacce karamar hukuma domin horar dasu a matsayin ‘yan sa kai ta yadda za su taimaka wajen kare al’ummar garuruwansu da kuma hada kai da jami’an tsaro wajen dakile ayyukan ‘yan fashin daji.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Mukhtar Adamu Bawa ya tattauna da daya daga cikin shugabannin dattawan na Katsina, Dr Bashir Kurfi wanda ke gaba-gaba wajen ganin an shawo kan matsalar, inda ya soma bayani a kan yadda suka ga girman wannan matsala.