Ko Man City za ta je ta doke Leipzig a Champions League?

An wallafa

RB Leipzig za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan farko zagayen 'yan 16 a Champions League da za su kara ranar Laraba a Jamus.

City ta kawo wannan gurbin bayan da ta yi ta daya a rukuni na bakwai da maki 14, Leipzig kuwa ta hada maki 12 ta yi ta biyu a rukuni na shida.

Sun kara a kakar bara a Champions League, City ta ci 6-3 a Etihad a Satumba, Leipzig ta yi nasara 2-1 a Disambar 2021.

City na fatan lashe Champions League a karon farko a tarihi, kofin da Pep Guardiola ke fatan dauka a kungiyar Etihad.

City na sa ran taka rawar gani, bayan da ta tashi 1-1 ranar Asabar a Premier League a gidan Nottingham Forest.

Arsenal ce ta daya a teburin Premier da maki 54 da tazarar biyu tsakaninta da City mai rike da kofin bara.

Kociyan Leipzig, Marco Rose ya kwan da sanin zai fuskanci Erling Haaland, wanda ya ci kwallo 32 a City a bana.

Rose ya yi aiki da Haaland a Borussia Dortmund, saboda haka zai yi kokarin ganin Haaland bai yi musu illa ba.

Da kyar idan Christopher Nkunku zai buga wa Leipzig gumurzun. Dan wasan tawagar Faransa ya ci kwallo 17 a dukkan fafatawa a bana.

Kwanan nan ya koma taka leda, bayan jinya raunin da ya ji a Nuwamba, wanda ya hana shi buga kofin duniya a Faransa.

Ya buga Bundesliga ranar Asabar ya bayar da kwallo an zura a raga a karawar da Leipzig ta ci Wolfsburg yana ta kokarin ganin ya fuskanci City ranar Laraba.

Wasa da aka buga tsakanin Leipzig da Man City:

2021/2022 Champions League

  • RB Leipzig 2 - 1 Man City

Champions League

  • Man City 6 - 3 RB Leipzig