Motocin da za a raba wa ƴan majalisa bashi ne - Gagdi

Motocin da za a raba wa ƴan majalisa bashi ne - Gagdi
An wallafa

A lokacin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan tashin farashin sufuri da na kayan masarufi, wani ɗan majalisar wakilai na Najeriya, ya mana ƙarin haske game da amfanin cire tallafin man fetur da gwanmatin ta yi.

Yusuf Adamu Gagdi wanda ɗan majalisa ne mai wakiltar mazaɓar Pankshin da Kanam da Kanke daga jihar Filato ya kuma yi bayani kan motocin da ake shirin saya wa ƴan majalisar, lamarin da ya janyo zazzafar muhawara a Najeriya.