Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa zai fuskanci kalubale tsakanin Guardiola da Amorim a Etihad?
Sabon kociyan Manchester United, Ruben Amorin zai kai wa Pep Guardiola ziyara a babban wasan hamayya na ƙungiyoyin Manchester.
Ranar Lahadi za a kece raini tsakanin Manchester City da Manchester United a Etihad a Premier League.
City mai rike da kofin bara ta yi nasara ɗaya daga wasa 10 baya da ta buga a dukkan fafatawa daga ciki aka doke ta bakwai.
Hakan ya sa City ta yi kasa zuwa mataki na biyar a teburi da tazarar maki tara tsakani da Liverpool mai jan ragama, mai kwantan wasa.
Shi kuwa Amorim ya yi nasara uku a karawa shida a dukkan fafatawa, sai dai an doke United karawa biyu a jere a hannun Arsenal da kuma Nottingham Forest a Premier.
Hakan ya sa United wadda ke fatan komawa kan ganiya karkashin sabon koci ta yi kasa zuwa mataki na 13 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
A cikin watan Nuwamba, Amorim ya doke City 4-1 a Champions League a Portugal lokacin da yake jan ragamar Sporting.
Wasan da aka buga a bayan nan tsakanin City da United:
Community Shield Asabar 10 ga watan Agusta 2024
- Man City 1 - 1 Man Utd
English FA Cup Asabar 25 ga watan Mayu 2024
- Man City 1 - 2 Man Utd
Premier League Lahadi 3 ga watan Maris 2024
- Man City 3 - 1 Man Utd
Premier League Lahadi 29 ga watan Oktoba 2023
- Man Utd 0 - 3 Man City