Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Bakura Abdusawi
Ku San Malamanku tare da Sheikh Bakura Abdusawi
An wallafa
Wannan mako a cikin shirin Ku San Malamanku mun kawo muku tattaunawa tare da Sheikh Musa Muhammad Umar, wanda aka fi sani da Bakura Abdusawi.
Malamin, wanda aka haifa a garin Banki na jihar Borno ya rasa idonsa ne tun yana ɗan wata huɗu da haihuwa, sai dai wannan bai zamo masa cikas wurin neman ilimi ba.