Har yanzu ina da ƙwarewar taimaka wa Arsenal cin kofi - Sterling

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwsan gaba na Arsenal Raheem Sterling ya ce "har yanzu yana da babbar rawar takawa" a yunƙurin da ƙungiyar ke yi na lashe kofi a kakar wasa ta bana, bayan ya taimaka mata kaiwa zagayen kwata fayinal na Champions League.
Yanzu ƙungiyar ta arewacin Landan za ta fafata da Real Madrid a gasar ta zakarun Turai.
Sterling ya bayar an ci ƙwallo biyu a wasan da Arsenal ɗin ta tashi 2-2 ranar Laraba, amma kuma ta doke PSV Eindhoven 9-3 gida da waje.
A wasan ne kuma ya zama ɗanwasan Ingila na farko a tarihi da ya saka hannu wajen ci wa ƙungiyoyi huɗu daban-daban ƙwallo a Champions League.
Yanzu ɗanwasan mai shekara 30 ya taimaka wajen cin 46 a gasar (ya ci 27, ya bayar an ci 19), inda David Beckam (52), da Harry Kane (50) da Wayne Rooney (47) ne kaɗai suka ɗara shi.
"Abin farin ciki ne in ga ina taimaka wa kulob ɗin," kamar yadda Sterling ya faɗa wa TNT Sports.
"Na san irin ƙwarewar da nake da ita. Kawai dai ina so na ci gaba da buga wasa. Ina babban kulob mai manyan 'yanwasa, kawai lokacina nake jira. Abin da nake yi kenan."
Duk da kasancewarsa wanda ya fi kowa taka rawa a wasan na PSV, Sterling bai buga wasu wasannin kirki ba tun bayan komawarsa daga Chelsea a watan Agusta a matsayin aro.
Rabon da ya ci ƙwallo tun watan Satumba, lokacin da suka yi nasara 5-1 a kan Bolton a gasar Carabao Cup.
Wasan na PSV ne karo na uku kacal da aka fara da shi a kakar wasa ta bana a Champions League, yayin da duka karawar Premier League 12 da ya buga yana shigowa ne daga benci.












