Mbappe ba zai buga wa Real wasan Getafe ba

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid za ta fafata a gidan Getafe a wasan mako na 34 a gasar La Liga ranar Laraba a Coliseum.

To sai dai Real Madrid za ta buga wasan ba tare da Kylian Mbappe ba, wanda ya ji rauni a wasan da Arsenal ta ci Real 2-1 a Champions League a Etihad.

Tuni Gunners ta yi waje da Real Madrid daga gasar zakarun Turai ta bana da cin 5-1 gida da waje.

Mbappe, ƙyaftin ɗin tawagar Faransa ya kammala hutun dakatarwa wasa ɗaya, sakamakon jan katin da aka yi masa a gidan Alaves ranar 13 ga watan Afirilu a La Liga.

Kenan bai buga wa Real wasan da ta doke Athletic Bilbao ba 1-0 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ranar 20 ga watan Afirilu.

Real za ta fafata da Getafe, bayan da take ta biyun teburi da tazarar maki bakwai tsakani da Barcelona ta ɗaya, wadda ta ci Real Mallorca 1-0 ranar Talata.

Getafe tana ta 12 a teburin La Liga da maki 39, kenan tana fatan shiga gurbin waɗan da za su wakilci Sifaniya gasar zakarun Turai a baɗi, amma da jan aiki a gabanta.

Bayan wasan da Real za ta kara da Getafe a La Liga ranar Talata daga nan za ta kece raini a wasan karshe da Barca a Copa del Rey ranar Asabar 26 ga watan Afirilu.

Ana sa ran Mbappe zai warke da wuri, domin ya fuskanci Barcelona a wasan hamayya na El Clasico na uku da za su fafata a tsakaninsu a bana.

Tuni Real Madrid ta sanar da ƴan wasan da ta je da su Getafe:

Ƴan wasan Real Madrid:

Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger da kuma Asencio.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Endrick, Brahim da kuma Gonzalo.