Gane Mini Hanya: Kan ciwon ƙoda

Bayanan sautiLatsa alamar da ke sama domin sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Kan ciwon ƙoda
An wallafa

A Najeriya, da an yi zancen ciwon ƙoda, babban abin da ke zuwa zuciyar mutum shi ne jihohin Yobe da Jigawa, saboda garuruwansu da ake ganin cutar ta yi katutu a can.

La'akari da girman matsalar da kuma yadda cutar ke matuƙar buƙatar kuɗi ne ya sa hukumomi suka ɓullo da tsarin yi wa masu larurar wankin ƙoda kyauta.

Haka zalika a jihar Yobe an ƙaddamar da wani gagarumin bincike don gano abin da ya sa cutar ta zama ruwan dare a yankin Bade.

Ga rahoto na musamman da Zahraddeen Lawan ya haɗa mana: