Ta yaya arahar masara za ta shafi manoma a daminar bana?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Manoman a Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa a kan abin da suka kira koma bayan da ake ta samu na noman masara da shinkafa a kasar, lamarin da suka ce yana barazana ga makomar sana'ar su.

Sun koka da tsadar kayan aikin gona, da kuma shigar da masara da shinkafa da ake yi cikin Najeriya daga ƙasashen waje.

Manoman sun bayyana fargabar cewa lamarin zai haifar masu da gagarumar asara a kakar bana, saboda haka kuma mafi yawansu ba za su iya noma masara da shinkafa ba a daminar baɗi, al'amarin da suka ce zai iya haifar da ƙarancin waɗannan kayan abinci, da kuma janyo yunwa a kasar.

Ƙungiyar manoman da suke harkar noma a matsayin sana'ar da suka dogara da ita kacokan a Najeriya, wadda a Turance ake kira Professional Farmers' Association of Nigeria, na cikin rukunin manoman da ke bayyana wannan damuwa.

Shugaban kuniyar na kasa, Hassan Sani Indabawa ya ce noma musamman na masara da shinkafa ya afka cikin tsaka mai wuya a Najeriya.

Ya ce ''Sama da shekara 40, aikin noma bai taɓa samun matsala kamar wannan halin da muke ciki ba. Daga kakar bara ya zuwa yanzu kenan.

''Watau karyewar farashin abubuwan da muke nomawa, musamman masara da shinkafa, da kuma tsadar kayayyakin noman musamman taki da abubuwan ƙwadago , musamman harkokin tan-tan, tsadarsu ta wuce tunani ta yadda noman babu riba kwata-kwata.'' In ji Indabawa.

Ya bayyana cewa su a matsayin su na manoma wannan ba ƙaramar matsala bace, wadda ta samo asali ne daga wasu matakan da gwamnatin Najeriya ta ɗauka.

Ya ce ''Gwamnatoci sukan daƙile da haramta shigo da kayayyakin abinci don bunƙasar na cikin gida, amma ita wannan gwamnatin sai ta bada dama, harma ta cire haraji da dukkanin kuɗin da ake karɓa ga wanda za su shigo da abinci.''

Shugaban ƙungiyar manoman ya ce suna da fargabar cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, to mutane da yaw aba za su iya yin noma ba a shekara mai zuwa saboda sun tafka asarar da bas u taɓa yi ba a rayuwar su.

Ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi ''ƙoƙarin farfaɗo da abin da ake nomawa na cikin gida, kuma a tunkari harkar tsaro, gwamnati ta canza manufofinta.''

Sai dai yayin da BBC ta tuntuɓi Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ƙaramin ministan aikin gona ta Najeriya, ya bayyana mana cewa ma'aikatar ba ta da masaniya a kan abincin da aka shigo da shi.

''Na san lokacin da shekarar can da ta wuce da aka samu ƙarancin abinci ko kuma abinci ya yi tsada, an yi maganar a buɗe ɗan window wanda za a shigo da shi (kayan abinci) saboda kamfanoni masu sarrafa waɗannan abubuwa ɗin za sus amu abin da za su sarrafa.'' In ji Sanata Sabi Abdullahi.

Ya ce dabarar gwamnati ta yin hakan ita ce karkatar da masu sayen amfanin gona domin sarrafawa, ta yadda za su shigo da kayan nasu daga ƙasashen waje domin sakin mara ga manoman cikin gida waɗanda ake fatan su iya wadata ƙasa da abinci.

Ministan noman na Najeriya ya ce ma'aikatarsa ta fara aikin duba yadda za a tsara dabarun ƙayyade farashin kayyakin aikin noma a ƙasar.

Hankalin manoma da sauran jama'ar ƙasa dai yana nan kan irin abin nan da aka ce,wa gani a kas, game da irin wannan alwashi da gwamnatin Najeriya ke ta bayarwa.