Shugaba Tinubu ya sauya Najeriya - Mohammed Idris
Shugaba Tinubu ya sauya Najeriya - Mohammed Idris
An wallafa
Yayin da shugaba Tinubu na Najeriya ke cika shekaru biyu na mulkinsa, ministan labarai na ƙasar, Mohammed Idris ya nemi ƴan Najeriya su ƙara haƙuri dangane da wahalhalun da suka sha domin a cewarsa al'amura za su yi sauƙi nan gaba.
Ministan ya ce lallai akwai wasu sassan da ke son gyara, amma kuma ya lissafa abubuwa guda biyu da ya ce sun sauya Najeriya.



