Kano Pillars ta je ta raba maki da Lobi Stars

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Lobi Stars da Kano Pillars sun tashi 2-2 a wasan mako na 13 a Premier League da suka kara ranar Asabar a Makurdi.

Tun a minti na bakwai da take leda Lobi ta fara zura ƙwallo ta hannun John Victor daga baya Liman Amadou ya kara na biyu minti bakwai tsakani.

Sai da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Pillars ta farke a karawar da aka yi a filin wasa da ke Lafiya.

Rabi'u Ali ne ya farke ta farko daga baya Mustapha Umar ya ci na biyu minti biyu tsakani, hakan ya sa Lobi da Pillars suka raba maki a tsakaninsu.

Kenan Pillars mai maki 19 tana ta shidan teburi, ita kuwa mai masaukin baƙi, Lobi mai maki 13 tana ta 16, bayan da suka yi wasan mako na 13.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi ranar Asabar:

  • El Kanemi Warriors 1-1 Akwa Utd
  • Niger Tornadoes 0-0 Ikorodu City
  • Bendel Ins 3-2 Kwara Utd
  • Heartland 0-0 Enugu Rangers

Wasannin da za a buga ranar Lahadi:

  • Katsina United da Remo Stars
  • Plateau United da Nasarawa United
  • Rivers United da Abia Warriors
  • Shooting Stars da Bayelsa United