Slot ya ci wasa biyu a jere a Liverpool a Premier League ta bana

Arne Slot

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sabon koci, Arne Slot ya ja ragamar Liverpool ta doke Brentford 2-0 a wasan mako na biyu a Premier League ranar Lahadi a Anfield.

Liverpool ta fara cin ƙwallo ta hannun Luiz Díaz a minti na 13 da take leda, kuma haka suka je hutu, ƙungiyar Anfield na cin 1-0.

Diaz ya ci ƙwallon a wasa na 100 da ya buga wa Liverpool kenan, tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Porto a 2022.

Saura minti 20 a tashi daga wasan ne, Liverpool ta ƙara na biyu ta hannun Mohamed Salah, ƙwallo na biyu a jere da ya ci a Premier League kenan.

Wannan shi ne karon farko da Liverpool ta buga wasa a Anfield ba tare da Jurgen Klopp ba, wanda ya yi murabus, bayan kammala kakar da ta wuce.

Klopp ya koma Liverpool daga Borussia Dortmund ranar 8 ga watan Oktoban 2015, wanda ya kammala aiki ranar 20 ga watan Mayun 2024.

Liverpool, wadda har yanzu ba ta ɗauki ɗan wasa ba a bana, ta kawo Arne Slot daga Feyenoord a kakar da ta wuce.

Liverpool ta fara kakar bana da cin Ipswich Town 2-0 a makon jiya, kenan ta ci ƙwallo huɗu a wasa biyu ba tare da an zura mata ko ɗaya a raga ba.

Liverpool za ta je Old Trafford ranar Lahadi 1 ga watan Satumba, domin buga wasan mako na uku a Premier League da Manchester United.

Brentford, wadda ta fara cin Crystal Palce 2-1 a wasan makon farko a Premier League, za ta je gidan Colchester ranar Laraba, domin buga League Cup.

Daga nan ne Brentford za ta karɓi bakuncin Southampton a wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar 31 ga watan Agusta.