UEFA ta hukunta Roma da Frankfurt

UEFA

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, UEFA ta hukunta Roma da Frankfurt, sakamakon halin rashin da'a da magoya baya suka nuna a watan Janairu a Europa League.

Roma ta kai zagayen cike gurbi, bayan doke Frankfurt a gida, yayin da ƙungiyar Jamus ta samu kai wa gurbi na biyu kai tsaye duk da rashin nasara.

Lokacin da aka yi hutu hatsaniya ta ɓarke a wajen zaman ƴan kallo da bai wa hammata iska tsakanin magoya bayan ƙungiyoyin biyu.

Sai dai jami'an tsaro da ma'aikatan sitadiya sun shiga tsakani da ta kai kurar ta lafa, har aka ci gaba da wasan zagaye na biyu ba tare da wata matsala ba.

An ci tarar Frankfurt Yuro 50,000, saboda magoya bayanta sun kunna abubuwan tartsatsin wuta da tayar da yamutsi da karin Yuro 5,000 kuɗin ɓata sitadiya.

Ita kuwa Roma za ta biya Yuro 30,000, an kuma umarci ƙungiyar za ta rufe wani sashen filinta a karawar gaba da za ta yi a gida.

Haka itama ƙungiyar Netherlands, FC Twente za ta biya tarar Yuro 35,000 da rafu wani sashen zaman ƴan kallo, saboda hatsaniyar da ta ɓarke a wasa da Besiktas.