Lafiya Zinariya: Illolin faɗuwa ga mai ciki 25/01/2025

Bayanan sauti
Lafiya Zinariya: Illolin faɗuwa ga mai ciki 25/01/2025
An wallafa

Faɗuwa ga mace mai ciki ba baƙon abu ba ne, domin a kan samu wasu matan masu juna biyu da hakan ta kan faru da su.

Baya ga dalilai na rashin lafiya da a wasu lokutan kan sanya mai ciki ta yanke jiki ta faɗi, wani lokaci zamewa ko gurɗewa kan sanya ta faɗi.

Haka kuma hatsari a kan abin hawa ko duka da hankaɗewa daga abokin zamanta sakamakon wani saɓani kan janyo mace ta faɗi a yayin da take da juna biyu.

Kuma yana da muhimmance mai juna biyu ta je asibiti domin tabbatar da lafiyarta da ta jariri bayan ta faɗi.

A cewar masana faɗuwar mace mai juna biyu yana da hatsari sosai, domin ya kan kai ga rasa rayuka.

Likitoci sun bayar da shawara kan wasu matakan da mace za ta iya ɗauka domin kaucewa faɗuwa, sai dai inda tsautsayi ya ratsa.

Wasu daga cikin abubuwan sune:

  • Daina sanya takalmi mai tsini ko mai tudu a yayin da mace ke da ciki
  • Kiyaye bi ta wuri mai santsi ko wuri mai tudu da kwari.
  • Riƙe hannun matattakala ko wani abu mai ƙarfi da ke kusa da zai hana ki kaiwa ƙasa.
  • Daina sanya takalmin da ƙarƙashinsa ke da santsi.
  • Yin tafiya a hankali.
  • Daina ɗaukar abubuwa masu nauyi, musamman waɗanda za su hana ki ganin gabanki.