Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Everton ta ɗaukaka ƙara kan cire mata maki 10
Kungiyar Everton ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke mata na kwashe mata maki 10 a gasar Premier saboda ƙarya dokar kasuwanci.
Wannan ne hukuncin mafi tsauri da hukumar Premier mai zaman kanta ta taba yanke wa wata kungiya a tarihin gasar.
Kungiyar ta shigar da koken ɗaukaka ƙarar ne gaban kwamitin shari’a a Premeir, yanzu kwamitin sauraron ƙararraki zai sanya ranar da za a saurari shari’ar.
Everton ba ta musanta karya dokar ba, amma ba ta yi tsammanin hukuncin zai yi tsauri ba kamar haka.
Za a saurari karar ne tare da yanke hukunci kafin kammala kakar wasanni ta bana.
“Kungiyar Everton yau ta shigar da kara gaban kwamitin shari’a na Premier kan hukuncin da hukumar Premeir mai zaman kanta ta yanke na kwashe wa kungiyar maki 10,” in ji Everton.
BBC ta gano cewa ba a sanar da kungiyar yadda aka cimma hukuncin cire mata maki 10 ba, kuma tana jin hukuncin da aka yi mata kan cinikayyar babu adalci ciki.
Za a karɓi ƙarar da ta ɗaukaka gaban kwamitin sannan sake bibiyar hukuncin da hukumar mai zaman kanta ta yanke, sannan a tabbatar da cewa hukuncin ya yi daidai ko kuma ya saba ƙa’ida.
Gabanin a cire mata makin tana matsayi na 14 amma da aka cire ta dawo matsayi na 19, wato ta biyun ƙarshe a Premier.