Juventus ta casa Sassuolo a wasan makon farko da fara Serie A ta bana

Asalin hoton, Getty Images
Juventus ta dura kwallo 3-0 a ragar Sassuola a wasan makon farko da fara kakar Serie A ta bana ta suka kara ranar Litinin.
Juventus ta ci kwallayen ta hannun Angel Di Maria da Dusan Vlahovic da ya ci a bugun fenariti, sannan ya kara na uku a wasan.
Juventus wadda ta yi ta hudu a kakar da ta wuce na fatan taka rawar gani a bana.
AC Milan ce ta dauki kofin bara a karon farko, tun bayan shekara 11, yayin da abokiyar hamayya Inter Milan ta yi ta biyu.
Wadanda za su wakilci Italiya a Champions League a bana sun hada da Milan da Inter da Napoli da kuma Juventus.
Juventus mai rike da kofin Serie A 36 jumulla, za ta ziyarci Sampdoria a wasan mako na biyu ranar 22 ga watan Agusta.
Ita kuwa Sassuolo za ta karbi bakuncin Lecce ranar 20 ga watan Agusta.







