Ɗan shekara biyun da yunwa ta kashe a idon mahaifiyarsa

    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Babban mai aikawa da rahotanni
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Dollow
  • An wallafa

Bayan shafe kwana biyu a wani ɗan ƙaramin asibitin Somaliya, Abdiwali Abdi ga alama yana ta faɗi-tashin samun sauƙi.

Jaririn ɗan shekara biyu har yanzu bai fi nauyin kilogiram 4.6 kawai ba - hakan dai bai fi nauyin wani lafiyayyen jariri sabuwar haihuwa ba.

Amma yanzu ya samu kuzari har yana iya gurnani, kuma mahaifiyarsa, Hawa, na zaune kusa da shi a kan gado a garin Dollow na kan iyaka.

Tana shayar da jaririyarta 'yar wata biyu tare da fatan shirin komawa sansaninsu na wucin gadi a wajen gari mai cike da ƙura.

"Akwai ƙwarin gwiwa," in ji Fatuma Mohammed, wata babbar ma'aikaciyar jinya kuma mai gudanar da harkoki 'yar ƙasar Kenyace.

Tana kai-komo a ɗakin da marasa lafiya ke murmurewa mai gado 17, ɗauke da jarirai guda 17 duka suna fama da rashin abinci mai gina jiki, da cututtuka iri daban-daban tare da su a nan cikin busasshen yankin kudancin Somaliya mai cike da rayuwar wahala, yayin da ƙasar ke fama da fari mai muni a cikin shekara 40.

"Ba mu da abincin da za mu ba shi, amma maƙwabtanmu suna taimaka mana," a cewar Hawa, 'yar shekara 22, tana zuba wa ɗanta ido.

Yana ta ramewa tsawon makwanni sakamakon cutar zazzaɓi da gudawa, kafin su zo nan don neman taimako.

Asibitin lardin Dollow - wani ɗan ƙaramin gari mai matuƙar ƙura a kan iyaka cikin yankin kudu maso yammacin Somaliya - sannu a hankali yana tallafa wa ƙananan yara kamar Abdiwali tsawon shekaru.

Da tallafin kuɗi daga gwamnatin Burtaniya da sauransu, an tanadi ma'aikatan al'umma da ke samar da tallafin aikin likitanci, ba kawai a garin ba, har ma a can cikin ƙauyukan da ke rikici, inda ƙungiyar masun iƙirarin jihadi ta al-Shabaab ke iko da ƙauyuka da yawa.

Sai dai a yau, bayan damuna ta biyar da ba a samu ruwan sama na a-zo-a-gani ba, sabbin masu zuwa neman magani sun cika Dollow.

Dubban iyaye kamar na Abdiwali - waɗanda shanunsu suka mutu kuma gonakinsu suka ƙeƙashe - sun taru a matsugunnai masu cunkoso, da fatan samun abinci da kuma wurin tsira.

"Muna magana ne a kan dubun dubatar rayukan da ke cikin hatsari kuma mutane a yanzu suna mutuwa.

Ba mu da wadatar kayayyakin da za mu tallafa musu," in ji Abdulkadir Mohamed, daga Majalisar kula da 'Yan gudun hijira ta Norway, lokacin da yake kallon ƙarin iyalan da ke isa ɗaya daga cikin manyan sansanoni.

A asibitin, kusan mata 100 ne ke zaune a cikin zafin tsakar rana, suna shayar da jariransu da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, suna jiran ganin cikowar jikinsu.

"Abubuwa sun yi matuƙar lalacewa a nan. Muna jin al'amura za su ci gaba da ƙazancewa - muna tsammanin nan ba da daɗewa ba za a ayyana shiga bala'in [yunwa]," a cewar Pamela Wasonga, wadda ke kula da shirin samar da abinci mai gina jiki a asibitin a madadin gidauniyar Trocaire ta Ireland.

Majalisar Ɗinkin Duniya tana gargaɗin cewa mutum miliyan 6.7 ne za su buƙaci tallafin abinci a Somaliya nan da 'yan watanni masu zuwa - kimanin kashi 40% na yawan al'ummar ƙasar.

A cikin dare ne rashin lafiyar Abdiwali ta ƙara tsanani. Jim kaɗan bayan ƙarfe tara na safiya da washe gari, sai yanayin zafin jikinsa ya yi matuƙar raguwa, cikin sauri kuma likitocin Somaliya suka lulluɓe shi da wani bargo mai ɗumi.

Gado biyu a tsakani, wata jaririya ce 'yar shekara ɗaya da rabi, ita ma ana ba ta irin wannan kulawa ta gaggawa.

"Gaskiya muna cikin damuwa. Jikin waɗannan yara ba ya iya sarrafa yanayin zafi sosai. Don haka ba ma ko kunna fankar saman ɗaki a nan.

Idan jikin yaro ya yi ɗumi, yiwuwar kuɓutarsa na da yawa," cewar Fatuma Mohammed, a lokacin da likita ya sa kwalbar auna zafin jiki a hammatar Abdiwali.

A yanzu, mahaifin yaron, Kerad Adan, ɗan shekara 28, ya isa asibitin kuma yana ta kai-komo cikin damuwa a zagayen gado.

Kafin wannan sabon fari, iyalinsa suna cikin ƙoshin lafiya da 'ya'yansu guda huɗu da shanu 40 da gidan bukkarsu a kusa da garin Qansax Dheere, mai nisan kilomita 200 kudu daga Dollow.

Sai dai a yankin, Bay, da ke can tsakiyar inda farin ya fi addaba kuma wata biyu da ya wuce saniyar da ta rage musu - wadda ita ce kafar samun duk kuɗin iyalin - ta mutu.

Jim kaɗan bayan nan, iyayen suka yanke shawarar tattara nasu-ya-nasu a kan amalanken jakuna suka nufi arewa da sauran 'ya'yansu, inda suka yi tafiyar ƙafa ta tsawon kwana shida.

Masu iƙirarin jihadi na ƙungiyar al-Shabaab sun yi yunƙurin hana su barin garin amma suka ƙwace wayar salular Kerad Adnan, suka farfasa ta a kan idonsa.

Kwatsam sai likitoci suka tattaru a kan Abdiwali. Ɗaya daga cikinsu ya yi amfani da yatsunsa biyu yana matsa ƙirjin yaron, yana ƙarawa da fatan zai fargar da zuciya ta ci gaba da bugawa.

Abokan aikinsa suka matsa kusa don ganin idanun yaron da suka ƙaƙƙafe. Iyayen jaririn suka tashi tsaye a jikin gado duk jikinsu a sanyaye.

Daga nan kuma, ƙarfe 10:13 da hantsi, sai rai ya yi halinsa.

"Zuciyar ta daina bugawa," Fatuma ta faɗa cikin raɗa, a yanzu tana kallon mahaifiyar Abdiwali lokacin da ta zame jiki daga kan gado ta fara kuka.

"Mun iya ƙoƙarin kuɓutar da dumbin jarirai. Amma mai yiwuwa lamarin yana daɗa taɓarɓarewa yanzu," cewar Fatuma Mohammed, a wani irin yanayi na mutumin da ya sha ganin irin wannan mutuwa.

"Abin babu daɗi kuma yana da ciwo ganin abin da za a iya hana shi faruwa kuma a iya gyara shi cikin sauri," in ji shugaban asibitin, Ali Shueb.

Cikin 'yan mintuna, mahaifin Abdiwali ya fara kiran waya, yana sanar da dangi da kuma shirin yin jana'iza da yammacin ranar.

"Duk mai rai sai ya ɗanɗani mutuwa," yana faɗa cikin sanyin murya, kamar yana faɗawa kansa.

Wata motar ɗaukar marasa lafiya ta dawo da baya a wajen asibitin, sai iyayen Abdiwali suka hau, cikin nutsuwa baban ya shigar da gawar ɗan nasa wacce aka nannaɗe a wani zane.

Daga baya Pamela Wasonga, ta nuna wa baƙi ɗakin shan magani na asibitin da ke maƙare da magunguna da kuma ɗan ƙaramin ɗakin gwaje-gwaje.

Tun a karon farko na farin daka yi ne a 2011 ta je Somaliya daga ƙasarta Kenya, kuma tun lokacin take nan, cike da ƙarin gwiwar cewa abubuwa da dama sun sauya, kuma kwalliya na biyan kuɗin sabulu.

"Ina ga aikin da aka ce ci gaba da yi tsawon lokaci a nan ya yi matuƙar kare afkuwar mummunan yaayi.

"Akwai ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama da na cikin ƙasa wadanda suke iya zuwa yankunan karkara masu wahalar shiga," ta ce.

Sai dai kuma a lokacin da ake shiga wani sabon yanayin na fari, asibitin ya yi asarar samun tallafi daga ƙasashen duniya saboda ɓata lokacin da ake samu a siyasance daga Mogadishu, babban birnin ƙasar.

Sannan kuma yanayin da ake ciki a duniya da ya ɗauke hankalin manyan ƙasashe ya sake sa wa ba a mayar da hankali kan bala'in da Somaliya ke ciki, inda sabbin bayanai ke nuna cewa ko rabin kuɗaɗen da ake buƙata don shawo kan masifar babu a ƙasa.

A lal misali, Birtaniya ta samar da fiye da dala miliyan 223 na taimakon jin ƙai a 2017 lokacin da Somaliya ta yi fama da fari.

A bana, kashi ɗaya bisa huɗu kawai ta bayar.

"Muna roƙon duniya... da kar su manta da Somaliya. Ƙasar na buƙatar taimako a yanzu.

"Idan ba mu samu ba, to za mu shiga cikin masifa, tabbas," in ji Ms Wasonga.

A lokacin da motar ɗaukar marasa lafiyan ta isa sansanin Ladan, a wajen garin daga gabashi, mutane sun taru a gaban tantin iyalan.

Iska ta kaɗa ta tayar da ƙura. An kawo ruwa a jarkoki don yi wa gawar wanka.

Dama tuni wani ya sayi farin ƙyalle don gabatar da jana'iza. Sai wasu maƙwabta biyu suka tona kabari.

Awa ɗaya bayan nan, sai Hawa ta isa maƙabartar. A al'adance, mata ba sa halartar jana'iza.

Amma ita da mahaifiyarta sun ce sam ba za a yi babu su ba, don haka suka zauna tare da wasu matan, kamar mita 20 daga inda kabarin yake.

"Kin yi ƙoƙarinki. Kina da wasu yaran." Kalaman da matan suka dinga gaya mata kenan don rarrashinta, yayin da baban Abdiwali da sauran amza suka dinga zuba ƙasa suna rufe kabarin.

Daga nan sai iyayen Abdiwali suka juya suka kama hanyar tafiya gida, yayin da iska ke ci gaba da kaɗawa tana kwasar datti yana lullɓe busassun ƙasusuwa da ƙayoyi.