Wasu Zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na 'yan yankin a wasu sassan duniya
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Dubban mutane sun taru a birnin Durban, na Afirka ta kudu ranar Asabar, domin ganin sabon sarkin Zulu Misuzulu kaZwelithini...
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ganin sabon sarkin shi ne abu na ƙarshe da ake gudanarwa a yayin bikin naɗin sabon sarki a ƙabilar ta Zulu
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Wasu 'yan makaranta a garin Giza na ƙasar Masar kenan, ke nuna ƙwarewarsu a rubutun Sinanci ranar Talata. Makarantar na ɗaya daga cikin makarantu 12 na ƙasar Masar da ke koyon harshen na Sinanci.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu matasa a birnin Cape Town na Afirka ta kudu ke wasan ninƙaya ranar Lahadi.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Masu kiɗan badujala ranar Talata a wajen wata maƙabartar manyan malaman addinin kirista a birnin Dakar na ƙasar Senegal.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Ana yi wa ranar laƙabi da ranar tunawa da manayan malaman, wanda mabiya addinin kirista ke bikin tunawa da ranar a sassa daban-daban na ƙasar.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Biki ne wanda 'yan ƙasar a ko'ina a fadin duniya ke girmama shi, kamar wannan matar mai suna Bolou Marie Marcele da ke zaune a ƙasar Ivory Coast, ta je domin saka fure a ƙabarin wata makusanciyarta.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Washe gari kuma magoya bayan tawagar kwallon kirket ta ƙasar Zimbabwe sun ɓarke da murna bayan da tawagar tasu ta yi nasara a kan ƙasar Pakistan a wasan kwallon kirket na duniya da ke gudana a ƙasar Australiya.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Ranar Lahadi, mabiya cocin Legio Maria da ke birnin Nairobi na ƙasar Kenya suka taru domin yin addu'o'in roƙon ruwa. Wasu sassan ƙasar da ma wasu ƙasashe yankin gabashin Afirka na fama da fari
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Washe gari kenan a ƙasar Yemen, inda wasu matasa 'yan ƙasar Habasha ke rawa a yayin wani gagarumin biki ma'aurata fiye da 4000
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A yayin da birnin Algiers ke shirin karɓar baƙuncin taron ƙasashen Larabawa , ranar Litinin an gudanar da raye-raye domin tunawa da juyin juya halin yankin ƙasashen Larabawa.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani manomi kenan cike da alfahari da kabewar da ya noma a gonarsa a yankin Sharqia na ƙasar Masar.