Amfanin kokomba ga lafiyar ɗan'adam
Kokomba da a wasu yankuna ake kira gurji na ɗauke da wasu abubuwan da ke inganta lafiyar jikin ɗan'adam.
Dakta Awwal Musa Umar ƙwararren masani a fannin kimiyyar cimaka da yadda ake amfani da cimaka wajen kare cutattukan da ke da alaƙa da cimar, ya ce kokomba na ɗauke da wasu manya-manyan abubuwa huɗu da ke taimakawa wajen inganta lafiyar jikin ɗa'adam kamar haka.
Ruwa: Ya ce kokomba na daga cikin kayan marmari da ke ɗauke ruwa mai yawa a jikinsa, ya ce kashi 95 na kokomba ruwa ne.
''Shi kuma ruwan na ɗauke da sinadarai masu matuƙar muhimmanci daga ciki akwai sinadarin alƙalai da ke daidaita gas ɗin da ke cikin mutum, wanda kuma yana taimakawa wajen kare kamuwa da cutar olsa ko gyambon ciki '', in ji shi.
Sinadaran rage sikari a jiki: Gurji na ɗauke da sidanaran da ke taimakawa wajen rage yawan sikari a jikin mutum.
"Ga masu ciwon suga idan sikarin da ke jikinsu ya yi yawa muna ba su shawara su riƙa markaɗa gurji suna shan ruwansa, ko su yawanta cinsa'', in ji likitan.
Ingantar garkuwar jiki da ƙawata kyau: Likitan ya kuma ce gurji ko kokomba kan taimaka wajen ingata sinadaran garkuwar ɗan'adam da kuma ƙawata kyawun mutum.
Daidaita hawan jini: Kokomba ko gurji na taimakawa wajen daidaita hawan jini ta hanyar cinsa a matsayin abinci, kamar yadda likitan ya yi bayani



