Muhimmancin rake ga lafiyar ɗan adam

Bayanan bidiyo, latsa sama don kallon bidiyon
Muhimmancin rake ga lafiyar ɗan adam
An wallafa

Kwararru a fannin cimaka sun ce rake na ƙunshe da wasu sinadarai da ke taimaka wa jikin ɗan'adam, musamman ma wajen gyara fatar jiki.

Ƙwararriya a fannin abinci, Zainab Iliyas Muhammad RDT, ta ce rake na kuma taimakawa mata lokacin al'ada musamman ma idan suka sha ruwansa.

Ta ce rake na ɗauke da sinadarin calcium, Vitamin B da kuma Iron, inda ta ce cikin waɗanda yake taimakawa har da yara.