PSG na zawarcin Osimhen

An wallafa

Paris St-Germain na iya neman sayen dan wasan Napoli Victor Osimhen, mai shekara 24 domin maye gurbin Kylian Mbappe wanda ake tunanin kungiyar za ta sayar da shi kafin kwantaraginsa ya kare a shekara mai zuwa.

Mbappe ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta barin PSG a kyauta idan kwantaraginsa ya kare a watan Yunin 2024.

Sai dai PSG na da burin sayar da shi a wannan bazarar idan har bai sanya hannu kan sabon kwantaragi da kungiyar ba.

Jaridar La Gazzetta dello Sport da aka buga ranar Lahadi ta tabbatar da cewa dan wasan na Najeriya ne zai zama kan gaba cikin wadanda PSG za ta yi zawarci domin maye gurbin Mbappe.

Idan cinikin Mbappe ya kankama a bazaran nan, hakan zai kara nauyin aljihun PSG, wanda zai iya ba su damar biyan bukatun da Napoli za su yi kan Osimhen.

Duk da sha'awar da PSG ke yi, Napoli na sa ran cewa za ta iya tsawaita kwantiragin Osimhen.

Idan har Osimhen zai sauya kungiya mai yiwuwa ya kai kusan fam miliyan 130, kodayake kwanan nan ya yi ikirarin bai damu ba ko ya zauna a Napoli ko a'a.