Pele: Janai'zar shahararren dan kwallon duniya cikin hotuna

An wallafa

A ranar Alhamis ne Pele ya mutu yana da shekaru 82, kuma tun lokacin ne ake ci gaba da alhinin mutuwar shahararren dan kwallon a fadin duniya.

Al'umma daga ko'ina a fadin Brazil da ma baki daga kasashen waje na ci gaba da jerin gwano tun ranar Litinin, don yin tozali da gawar Pele da aka girke a filin wasan Santos.

Baya ga Shugaba Lula da Silva da ya sha rantsuwa ranar Lahadi, Shugabanni a duniyar kwallon kafa da suka hada da na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino duka sun hallara a filin don yin ta'aziyya.

Ga wasu hotunan yadda jana'izar ke gudana.