Me Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa za su iya yi domin rage farashin mai a duniya?

Karin farashin mai na kara tsadar rayuwa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kasashe biyu da suka fi hako man fetur za su yi ganawa mai muhimmanci Laraban nan domin yanke shawara a kan adadin mai da za su kara a kasuwa daga watan Satumba.

Wannan ya biyo bayan ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ya kai yankin Gabas ta Tsakiya makonnin da suka wuce a yunkurinsa na shawo kan Saudiyya ta kara adadin mai da take hakowa domin rage farashinsa a kasuwar duniya.

Har yanzu ana cinikin danyen mai ganga 1 kan sama da $100 tun watan Fabrairu, lamarin da ya kara tsadar rayuwa a kasashe da yawa.

Me ya sa taron ke da muhimmanci?

Fadar White House na fatan kasashe 13 dake cikin Kungiyar Kasashe masu arzkin man fetur OPEC za su yanke shawarar kara adadin mai da suke sayarwa.

An kafa kungiyar a 1960 da nufin daidaita man da ake sayarwa a duniya da farashinsa.

Saudiyya ita ce kasar da ta fi yawan hako mai da ke kungiyar kuma bayan ganawa da Yarima Mohammed Bin Salman, Shugaba Biden ya ce yana kyautata zaton adadin man zai karu.

Sai dai jami’an Saudiyya sun jaddada cewa duk wata shawara da za a yanke dangane da karin adadin mai a kasuwa, sai an tattauna da Opec+.

Opec+ ita ce babban kungiyar kasashe masu arzikin mai 23, ciki har da Rasha, wadda ke ganawa kowane wata a birnin Vienna domin yanke shawara a kan adadin danyen da za a sayar a kasuwannin duniya.

'Ya'yan Opec Angola, Najeriya da Malesiya sun gaza samar da adadin man da aka bukaci su samar a wata daya.

Asalin hoton, Getty Images

Me zai sa farashin mai ya ragu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A baya a watan Afrilun 2020, Open+ ta ringa rage adadin mai da take sayarwa lamarin da ya share wa’adin annobar korona lokacin da bukatar man ya ragu. Tun 2021, kungiyar tana kara adadin man da take sayarwa a hankali.

A wajen taron kungiyar na karshe, Opec+ ta yanke shawarar kara adadin gangar mai da take samar wa dan kadan a watan Agusta.

Sai dai kawai kunna kan fanfon mai ba zai yi saukin da ake tunani ba. A kan takarda, wasu kasashen da ke cikin kungiyar kamar Angola da Najerya da Malaysia na fama wajen samar da adadin da aka yanke musu a wata daya.

A daidai wannan lokaci kuma man da Rasha take samarwa ya ragu saboda takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakaba mata.

Rasha ita kuma ta kara adadin man da take sayarwa zuwa kasashen Asia kamar China da Indiya.

Kasar ta tafi kowacce tagomashi Saudiyya tare da makwabciyar ta UAE su ne kasashe biyu kacal da za su iya kara adadin man da suke fitarwa.

Saudiyya za ta ringa fitar da gangar mai miliyan 11 a watan Agusta, lamarin da kwararru a harkar makamashi suke gani na da yawa sosai, kuma haka ya sa ba za ta iya kara adadi mai yawa ba.

“Babbar damuwar Saudiya da Opec+ shi ne akwai abubuwa da yawa da ba a sani ba. Babu wanda ya san yanayin kasuwar mai a watanni 6 masu zuwa ko a shekara mai zuwa,” a cewar Karen Young, babbar mai bincike a manazartar yankin Gabas ta Tsakiya da ke birnin Washington DC.

Fashin bakin kasuwa na zaton Shugaba Vladimir Putin na Rasha yana so farashin mai ya cigaba da tsada yadda zai cigaba da biyan kudin yakin Ukraine domin dakile tasirin takunkuman da kasashen yammacin duniya suka saka mata.

Ita kuma Saudiyya, hadin kai tsakanin ‘ya’yan kungiyar Opec+ shi ne ya fi muhimmanci, kuma za ta guje wa duk wata shawara da za ta kawo tsaiko.  

Kuri'ar jin ra'ayin mutane ya nuna cewa Joe Biden ya rage farin jini yayin da farashin mai fetur yayi tashin goron zabo

Asalin hoton, Getty Images

Me zai faru da farashin mai yanzu?

Opec ita da kan tana hasashen bukatar mai za ta karu a shekarar 2023 amma a hankali idan aka kwatanta da wannan shekara.

Masu fashin bakinta sun ce hakan na da alaka da cigaba da aka samu wajen dakile annobar Corona a China.

Hasashe daga Hukumar Makamashi ta Kasa da Kasa da Hukumar Bayanan Makamashi ta Amurka na nuna cewa za a cigaba da samun karuwar bukatar mai sosai, duk da cewa fargabar tauyewar darajar kudade a kasashe da dama da tsaiko wajen bunkasar tattalin arziki.

Hakan ya na nufin kasashen da ke fitar da mai za su iya samun kawunansu samar da adadin mai yawa da sauri a cikin shekaru biyar domin daidaita bukatar man da abin da kasuwa ta samar – lamari mai sarkakia, lura da rashin yanayin samar da hakan, da kuma rashin zuba jari wajen tace man.

Farashin man fetur a Amurka yanzu yayi sama, mafi tsada a shekaru 13 a wannan shekara.

Amurka za ta saki misalin ganga miliyan 1 a rana daga rumbun mai da ta adana tun watan Afrilu – a matsayin daya daga cikin matakan ta na zuba ganga miliyan 180 a kasuwa a cikin watanni 6  dake kawo karshe a karewar watan Oktoba.