Matasa su yi karatun ta-nutsu - Sardaunan matasan sakkwato

Bayanan bidiyo, Hira da Sardaunan matasan Sakkwato
Matasa su yi karatun ta-nutsu - Sardaunan matasan sakkwato
An wallafa

Alhaji Mujitapha Isa, Sardaunan matasan Sakkwato ya yi kira ga matasan Najeriya da cewa lokacin siyasa ya fara, dan haka su yi karatun ta-nutsu, kada su bari a yi amfani da su wajen biyan buƙatun 'yan siyasa, kada su zama 'yan bangar siyasa.

Sannan kuma Garkuwan Matasan Arewacin Najeriyan ya yi kira ga 'yan siyasar ƙasar da cewa su ji tsoron Allah ga dukkanin al'amuransu, su sani cewa Allah shi ke bayar da mulki ga wanda ya so.

Kada su yi amfani da abin hannunsu domin bai wa matasa su yi shaye-shaye domin yin ta'addanci don cimma muradunsu na mulki, su sani cewa hakan zai shafe su daga baya.