Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fifa ta dakatar da Rubiales shekaru uku
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa ta dakatar da tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya Luis Rubiales shekaru uku.
Rubiales ya sumbaci 'yar kwallon Sifaniya, Jenni Hermoso a leɓe bayan wasan ƙarshe na cin kofin duniya na mata da Sifaniya ta doke Ingila a Sydney.
Hermoso ta ce ya sumbace ta ba tare da amincewarta ba, hakan ya haifar da ce-ce-kuce, inda a ƙarshe Rubiales ya sauka daga muƙaminsa a watan Satumba.
Daga baya Hermoso ta shigar da ƙara a kan Rubiales.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne Fifa ta sanar da dakatar da Rubiales na tsawon shekaru uku saboda karya dokar da'a ta 13 ta dokokinta.
Ta tabbatar da lamarin ya shafi "abubuwan da suka faru a lokacin wasan ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta mata ta Fifa ranar 20 ga watan Agustan 2023, wanda aka dakatar da Mista Rubiales na wucin gadi na tsawon kwanaki 90".
Rubiales na da damar ɗaukaka ƙara idan har bai amince da hukuncin da aka yanke masa ba.