Real za ta kara da Osasuna a wasan karshe a Copa del Rey

An wallafa

Real Madrid za ta fuskanci Osasuna a karawar karshe a Copa del Rey ranar 6 ga watan Mayu.

Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama na neman Copa del Rey na 20 a karawar da za su yi a filin wasa La Cartuja, wato na Sevilla.

Ranar Laraba, Real Madrid ta kai wasan karshe bayan da ta doke Barcelona 4-0 a Nou Camp a wasa na biyu a daf karshe.

Karim Benzema ne ya ci uku rigis, sai Vinicius Junior, wanda shine ya fara zura kwallo a ragar Barcelona.

A wasan farko a zagayen daf da karshe, Barcelona ce ta yi nasara da cin 1-0 a Santiago Bernabeu cikin watan Maris.

Osasuna ta kai wannan matakin bayan da ta fitar da Athletic Bilbao, karon farko da za ta buga wasan karshe tun 2005.

A wasan karshe da Osasuna ta buga a Copa del Rey a kakar 2004/5, Real Betis ce ta lashe kofin da cin 2-1.

Real Betis ce mai rike da kofin bara, amma ba ta kai labari ba a kakar bana.

Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, sai Athletic Bilbao mai 23 da kuma Real Madrid mai 19 - Osasuna ba ta daukar kofin ba.

Barcelona da Real Madrid sun buga El Clasico karo biyar a bana, inda kungiyar Nou Camp ta yi nasara a wasa uku ta Santiago Bernabeu ta ci biyu.

Wasa biyar tsakanin Barcelon da Real Madrid a bana:

Copa del Rel Laraba 5 ga watan Afirilun 2023

  • Barcelona 0 - 4 Real Madrid

La Liga Lahadi 19 ga watan Maris 2023

  • Barcelona 2 - 1 Real Madrid

Copa del Rey Alhamis 2 ga watan Maris 2023

  • Real Madrid 0 - 1 Barcelona

Sifanish Super Cup Lahadi 15 ga watan Janairun 2023

  • Real Madrid 1 - 3 Barcelona

La Liga Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022

  • Real Madrid 3 - 1 Barcelona

Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.

Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta karbi bakuncin Villareal a wasan La Liga, kwana hudu tsakani ta kece raini da Chelsea a quarter finals a Champions League a Sifaniya.

Ranar Litinin 10 ga watan Afirilu Barcelona za ta kece raini da Girona a La Liga a Nou Camp.