Waiwaye: Faɗuwar Tinubu a filin taro da hana hawan sallah a Kano

An wallafa

Wannan maƙala ce da ke kawo maku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

'Yan sanda sun hana hawan Sallah a Kano

A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al'ada a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan babbar sallah da za a soma ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami'anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.

''Haka kuma an haramta duka nau'ikan hawan sallah a lokacin bukukuwan babbar sallah da ke tafe'', in ji sanarwar.

Tinubu ya zame a Eagles Square a ƙoƙarin hawa mota

Duk dai a cikin makon da ya gabatan, fadar shugaban Najeriya ta sanar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu "yana cikin ƙoshin lafiya bayan faɗuwa da ya yi kafin jami'an da ke tare da shi su tallafo shi" sakamakon zamewa lokacin hawa mota.

Bola Tinubu mai shekaru 72, dai na ƙoƙarin hawa mota ƙirar a-kori-kura wadda za ta zagaya da shi a dandalin Eagles Square inda ake taron ranar dimokaraɗiyya, sai ya zame.

Mataimakin Shugaba Tinubu na musamman kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya ce " ƴar ƙaramar zamiya ce. Kuma dandanan (Tinubu) ya miƙe ya ci gaba da zagaya dandalin da ake bikin. Babu wata matsala."

Daga bisani an ci gaba da fareti inda shugaban ya tsaya a cikin motar yana gaisawa da jama'a.

Ƴan bindiga sun 'kashe mutum 50' a jihar Katsina

Aƙalla mutum 50 aka kashe sannan aka sace wasu da ba a san adadinsu ba sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Mazauna garin Yargoje sun faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa maharan sun afka wa ƙauyen ne tun ranar Lahadi da dare.

Gomman 'yanfashi ne suka kutsa ƙauyen da ke ƙaramar hukumar Kankara, inda suka fara harbi a kan mai tsautsayi.

"Sun yi ta harbi a kan kowa da kowa, inda suka kashe mana mutum 50 ciki har da ƙanina," kamar yadda Hassan Ya’u ya bayyana ta waya.

Wani mazaunin Kankara mai suna Abdullahi Yunusa ya ce da kyar ya tsallake rijiya da baya, kuma hare-haren sun ci gaba har zuwa tsakar dare.

"Sun mayar da ƙauyenmu wani filin kisa, kusan babu gidan da harin bai shafa ba," in ji shi.

Ƴan majalisa sun nemi a koma tsarin mulki na wa'adin shekara shida

A cikin makon jiyan dai Majalisar wakilan Najeriya ta fara muhawara kan wasu kudurori da ke neman komawa ga tsarin yin wa'adin mulki guda na tsawon shekara shida ga shugaban kasa da gwamnoni da kuma shawawar samar da mataimakan shugaban kasa guda biyu daga bangaren arewaci da kudancin kasar

Tuni wadannan kudirorin suka tsallake karatu na daya a Majalisar wakilai, inda ake sa ran za a ci gaba da tafka muhawa har sai an musu karatu uku, kafin aikawa majalisar dattawa ita ma ta yi na ta aikin.

Wasu 'yan majalisar wakilai 35 ne suka taso da batun, inda suke ganin cewa zai taimaka wajen ceto kasar daga halin da take ciki.

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

A ranar Alhamis ne kuma Sojojin Najeriya suka ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30..

Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina

Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina.

Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da 'yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi.

Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi ƙaurin suna wajen kai hare-haren satar shanu da safarar makamai, da tashe-tashen hankula a jihohin arewacin ƙasar da dama.