Alamomin kamuwa da lalurar shanyewar ɓarin jiki

Alamomin kamuwa da lalurar shanyewar ɓarin jiki
An wallafa

Shanyewar ɓarin jiki wata matsala ce jama'a ke fama da ita a wannan zamani.

Al'amarin ya kai ga masu ƙarancin shekaru kan samu wannan larura.

Alƙaluma sun nuna a kan iya samun mutum ɗaya a duk cikin mutum 10 da ka iya samun wannan lalura.

Dakta Anisa Ambursa likita ce a Abuja ta kuam shaida wa BBC cewa ana iya gadon wannan cuta sannan kuma ana iya samun lalurar sakamakon yanayin tafiyar da rayuwar da mutane ke yi a wannan zamani.

Likitar ta kuma zayyana alamomin da za a gane mutum ana gab da kamuwa da shanyewar bangaren jiki.