...Daga Bakin Mai Ita tare da Zainab Ishola

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sma domin kallo
...Daga Bakin Mai Ita tare da Zainab Ishola
An wallafa

A wannan makon mun kawo muku tattaunawa da Zainab Ishola a shirinmu na ...Daga Bakin Mai Ita wadda jaruma ce a masana'antar fina-finai ta Kannywood.

Zainab wadda ƴan asalin jihar Borno ce amma ta tashi a birnin Jos sakamakon aikin mahafinta.

Jarumar dai tana da matakin karatu na difloma a fannin aikin jinya kuma yanzu tana ci gaba da digiri.

Shirin da Zainab ta fara fitowa a ciki shi ne fim ɗin 'Ina Mazan", wanda ta ce ta yi shi jikinta na ɓari duk da cewa ta kalli fim ɗin har na kwanaki biyu tana kallon sa.

Sai dai wani abun da Zainab ta ce yana ci mata tuwo a ƙwarya a masana'antar tasu shi ne tsegumi.

"Maimakon idan ka yi abu a same ka a gyara maka a matsayinka na ɗa ko jika ko kuma ɗan uwa amma sai aje an zauna a yi ta maganarka."