Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An raba maki tsakanin Real da Atletico a La Liga
Real Madrid da Atletico Madrid sun tashi 1-1 a gasar La Liga karawar mako na 23 da suka fafata a wasan hamayya ranar Asabar a Santiago Bernabeu.
Atletico ce ta fara cin ƙwallo a bugun fenariti ta hannun Julian Alvarez tun kan hutu, haka suka je hutu an zura 1-0 a ragar Real Madrid.
Daga baya ne Real Madrid ta farke ta hannun Kylian Mbappe, kuma na 23 da ya ci kenan a dukkan karawa a bana a Real Madrid.
Wannan shi ne karo na biyu da suka kece raini a tsakaninsu a gasar, sun tashi 1-1 a Atletico a babbar gasar tamaual ta Sifaniya ranar Lahadi 29 ga watan Satumba.
Wannan shi ne karon farko da suka kara a wasan na ƴan birnin Madrid a 2025, kuma na farko da Mbappe ya yi a fafatawar ta hamayya.
Da wannan sakamakon Real Madrid ce kan gaba a teburin La Liga da tazarar maki ɗaya tsakani da Atletico ta biyu mai maki 49.
Ranar Talata 11 ga watan Fabrairu Real Madrid za ta je Manchester City, domin buga wasan cike gurbi a Champions League.
Ita kuwa Atletico Madrid za ta karɓi bakuncin Celta Vigo a wasan La Liga ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu.
Ƴan wasan Real Madrid da suka fuskanci Atletico:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin, Sergio Mestre.
Masu tsare baya: Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Mendy, Jacobo, Asencio, Lorenzo.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim, Gonzalo.