Ko tsufa na kawo makanta?
Ko tsufa na kawo makanta?
An wallafa
Albarkacin makon yaƙi da cutar Glaucoma ta Duniya, Dakta Aisha Sheriff Kalambe ta faɗi yadda za ku iya gane ko kuna da Glaucoma mai janyo makanta.
Cuta ce wadda ke haifar da makanta, ana iya magance cutar kafin ta yi ƙamari, amma kuma idan makantar ta riga ta faru to ba za a iya magance ta ba – in ji likita.
Ta yaya za ku gane cewa kuna cikin haɗarin kamuwa da 'Glaucoma', mene ne ke haifar da ita, ta yaya za ku kare kanku?



