Tarihin ƙarin farashin mai a Najeriya

Tarihin ƙarin farashin mai a Najeriya
An wallafa

BBC ta yi nazari kan tarihin ƙarin farashin man fetir a Najeriya.

Mun yi diba ne tun daga 1999 zamanin mulkin Cif Olusegun Obasanjo zuwa yanzu 2024 zamanin mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Farashin litar mai ya ci gaba sauyawa a Najeriya daga N22 a 1999 zuwa N897 farashin gwamnati a 2024.

Najeriya mai yawan al'umma a Afirka, tattalin arzikinta na dogaro ne da arzikin mai, kuma tsadar man a Najeriya kan yi tasiri kan harakokin rayuwa a ƙasar.