Yadda yajin aikin wata uku ya sauya tunanin ɗaliban firamare a Abuja
Yadda yajin aikin wata uku ya sauya tunanin ɗaliban firamare a Abuja
An wallafa
Watanni uku kenan makarantun firamare a babban birnin Najeriya, Abuja suke kasance a rufe sakamakon yajin aikin da malamansu ke yi.
Malaman makarantar na Abuja dai na neman gwamnati ta biya musu wasu buƙatunsu da suka haɗa da aiwatar da albashi mafi ƙanƙanta na 70,000 da biyan su albashin da suke bi.
Al'amarin ya janyo ƙungiyoyi masu raji sun yi zanga-zangar yin kira ga gwamnatin tarayya ta saurari ƙorafe-ƙorafen malaman domin komawar ɗalibai azuzuwansu.



