Shawarata ga matasa masu burin shiga gwamnati - Khalil Nur Khalil

Shawarata ga matasa masu burin shiga gwamnati - Khalil Nur Khalil
An wallafa

Khalil Nur Khalil, mai bai wa gwamnan jihar Katsina kan tattalin arziƙi ya fara shiga gwamnati tun yana ɗan shekara 25, kuma matashin ya samu ɗaukaka inda har ya riƙe shugabancin hukumar bunƙasa zuba jari ta jihar Kaduna a zamanin Mallam Nasir Elrufai.