'Yajin aikin ASUU ya ɓata min wata takwas na rayuwata'

An wallafa

Malaman jami'o'i a Najeriya sun ce za su koma bakin aiki ranar Litinin bayan yajin aiki na tsawon wata takwas da ya sa jami'o'in gwamnati kasancewa a rufe, abin da ya sa dalibai zaman gida cikin takaici da bacin rai.

"Wata takwas kenan da na yi asara a rayuwata, to kuma me yajin aikin ya cimma?" Tambayar da wata daliba ta yi kenan, wadda ba ta son a bayyana sunanta.

Yajin aikin da aka fara a watan Fabrairu shi ne na 9 a cikin shekara 13, kuma shi ne na baya-bayan nan a wannan dambarwa ta tsawon shekara goma kan batun samar da karin kudade ga manyan makarantun gaba da sakandire na kasar.

Babbar kungiyar malaman jami'o'i ta kasar ASUU, ta jima tana fafutuka domin ganin gwamnati ta kara kudaden da take bayarwa domin tafiyarwa da kuma bunkasa jami'o'i, amma gwamnatin na cewa ba ta da halin da za ta iya biyan dukkanin bukatun kungiyar.

ASUU ta ce ta dakatar da yajin aikin ne a matsayinta na kungiya mai bin doka da oda da kuma rokon da 'yan Najeriya ke yi mata, amma har yanzu ba a warware matsalolin da suka sa ta shiga yajin aikin ba.

Malaman sun dakatar da aikin koyarwa a jami'o'in gwamnati a kan bukatun nasu, to amma yajin aikin da aka shafe tsawon lokaci ana yi ya haddasa damuwa sosai ga dalibai da iyayensu.

Wata daga cikin daliban da ke murnar komawa karatu ta ce, "Kusan ba abin da na yi tsawon wannan wata takwas.

''Mutane suna ta ce min in je in koyi sana'ar hannu, in je in koyi sana'ar hannu. To da ina son in koyi sana'a ai da ba zan je jami'a ba, '' in ji ta.

Ba a dai san yadda aka sasanta a kan ainahin abin da ya haddasa kiki-kaka a tsakanin bangarorin biyu ba, wato batun tsarin biyan malaman albashi, tun 2020.

Wannan ne ya sa ake ganin ba za a iya kawar da yuwuwar sake komawar malaman wani yajin aikin ba a nan kusa.

Malaman suna korafi ne da cewa tsarin biyan nasu bai kunshi wasu alawus-alawus ba kuma yana nuna bambanci a tsakaninsu.

Sai dai a nata bangaren gwamnatin ta kafe cewa tsarin zai taimaka mata kawar da ma'aikatan bogi.

Sannan kuma ta yi watsi da wata manhaja da malaman suka kirkiro saboda a cewarta manhajar ba ta tsallake gwajinta ba.

A watan Disamba na 2020 ne aka kawo karshen wani yajin aikin da suka yi a baya, bayan da gwamnati ta sanya hannu a wata yarjejeniya ta duba bukatun da kungiyar ta ASUU ta gabatar.

To amma kusan a iya cewa gwamnatin ta ja baya a kan wannan yarjejeniya, abin da ya sa kungiyar ta yi ta gargadin cewa za ta koma yajin aikin, abin da a karshe dai ta shiga a watan Fabrairu na wannan shekara.

Da wannan janye yajin aikin yanzu ana sa ran dalibai bayan sun rasa kusan shekara daya ta karatu, shekara biyu bayan da annobar korona ta haifar da cikas ga wata shekara daya ta karatun su koma aji ranar Litinin.

Kuma da yawa daga cikinsu ba sa jin dadi cewa ba za su kammala karatun ba a lokacin da ya kamata a ce sun gama.

Wata daliba a Jami'ar Patakwal ta koka da cewa, ''Abokan karatuna a jami'o'i masu zaman kansu tuni sun gama karatunsu yanzu sun sha gabana a rayuwar bayan karatu da shekara biyu.''

Yawan yajin aikin ya sa mutane da dama ba su da kwarin guiwa a kan karatun makarantun gaba da sakandire na gwamnati a Najeriya.

Wannan ne ya sa ma wasu suka gwammaje su je jami'o'i masu zaman kansu masu tsada ko kuma su tafi na wasu kasashe kamar na gabashin Turai masu saukin kudi.

Yawanci tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar kan ja lokaci to amma ta wannan shekarar ta fi daburcewa.

Abin da ya sa har gwamnatin ta kai karar kungiyar kotu, kotun da malaman suka yi watsi da umarninta na su koma aiki.

'Ya'yan 'yan siyasa da dama ciki har da na Shugaba Muhammdu Buhari da manyan farfesoshi yawanci suna tafiya kasashen waje ne karatu.

Wanda wannan na kara bata wa 'yan kasar rai cewa gwamnati da tsarin tafiyar da jami'o'in ba da gaske suke ba wajen samar da mafita mai dorewa a wannan rikici.

A makon da ya gabata Shugaba Buhari ya sanar cewa gwamnati za ta zuba Naira biliyan 470 (kwatankwacin Dala biliyan 1.1 ko Fam miliyan 960) a harkar jami'o'i a irin yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar, wanda hakan zai kai ga kara albashin malaman.

To amma kuma ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da daukar dawainiyar makarantun gaba da sakandire ba ita kadai.

Dole ne a dubo wani tsari da ya yi nasara na wasu kasashe a bi wajen samar da kudade ga bangaren, kamar yadda shugaban ya ce.

Yadda za a samar da kudaden gudanarwa ga makarantun gaba da sakandire ya kasance babbar matsala tsawon shekaru a Najeriya.

Kuma rashin yawan kudin makaranta da ake biya a makarantun gwamnati ya sa mutane da yawa neman shiga makarantun.

Sai dai kuma wannan na daga abubuwan da suka janyo malaman ba su da wani albashi mai yawa sosai da kuma rashin samar wa bangaren ilimin kudaden gaske.

Kwararru na ganin hanya daya ta magance wannan matsala ita ce a ba wa jami'o'in 'yancin cin gashin-kai su kara kudi, wanda hakan zai sa su samu karin kudaden tafiyarwa.

To sai dai kuma a kasar da ake ganin yawancin iyalai talakawa ne kuma akwai miliyoyin yara da ba sa zuwa makaranta, ana fargabar cewa daukar wannan mataki ka iya bata abin ma gaba daya, lamarin ya fi yadda yake muni.

A baya an yi tunanin bullo da tsarin bai wa dalibai bashi mai kudin ruwa kadan, to amma malaman suka ki amincewa da shi.

A shekarar da ta gabata, shugaban kungiyar ta ASUU, Emmanuel Osodeke, ya yi korafi a kan wannan tsarin da cewa:

''Idan da mun yarda cewa dalibai su biya Naira miliyan daya a matsayin kudin makaranta, da wai sun kara mana yawan albashi, to kuma wa jama'a da dalibai za su zarga?"

"ASUU za su ce,'' in ji shi.

Haka kuma ASUU na son ganin gwamnati ta dakatar da kirkiro sabbin jami'o'i har sai ta iya samar da kudin tafiyar da wadanda take da su.

Sannan kuma ta fitar da rahoton kwamitin da ya yi bincike kan manyan shugabannin jami'o'in, wadanda kungiyar ke zargi da rashawa.

Sai dai 'yan Najeriya da dama na ganin kungiyar ta malamai na gaggawar shiga yajin aiki a kan bukatunta.

Da kuma zakewa kan wasu daga cikin bukatun, misali, yadda malaman ke kafewa cewa su za su gaya wa gwamnati yadda za ta rika biyansu albashi.

Wasu 'yan kasar na ganin cewa wannan abu ne da ya wuce gona da iri.

Bisa ga dukkan alamu gwamnati ta biyo wa kungiyar malaman ta bayan gida, inda ta yi rijistar wasu karin kungiyoyi biyu da ke zaman tamkar kishiyoyin ASUUn, domin rage mata karfi da kuma raba kai.

Kungiyoyin su ne, CONUA (Congress of Nigerian University Academics) da NAMDA (National Association of Medical and Dental Academics)

Daya daga cikin kungiyoyin, ta ce za ta yi aiki tukuru domin ganin cewa ba a sake jefa kasar cikin halin yajin aikin ba.

Wannan wata dabara ce da ta yi tasiri sosai ga gwamnatocin baya a kasar wajen kassara kungiyoyin kwadago masu karfin gaske, ta hanyar tilasta musu, su mika wuya a tattauna da su.

Idan har wannan dabara za ta sa jami'o'in su kasance a bude, to ba shakka dalibai da yawa da iyayensu za su so ta.

Ko da kuwa ba ta magance matsalolin da ake kai ruwa rana a kansu ba.

"Ina dai fatan wannan shi ne yajin aiki na karshe da zan fuskanta har na kammala jami'a. Amma dai fata da addu'a nake yi kawai," in ji wani dalibi da ya rubuta hakan a sakon waya.

"Saboda malaman da ake kira na ASUU ka iya dawowa su ci gaba da yajin aikin a nan gaba, su ce ba sa son albashinsu na yanzu, suna son kari.

To a nan me za mu yi? Babu," ya ce, inda ya yi amfani da hoton alamar mutumin da abu ya fi karfin sa.