Daga Bakin Mai Ita tare da Hadiza Kabara
Daga Bakin Mai Ita tare da Hadiza Kabara
An wallafa
Hadiza Muhammad Sani wadda aka fi sani da Hadiza Kabara ta ce ta soma sha'awar harkar fim ne bayan ta kalli wani fim mai suna 'Allura Da Zare'.
A tattaunawarta da BBC a shirin Daga Bakin Mai Ita Kashi na 25, Hadiza Kabara ta ce a lokacin tana yarinya ita mace ce mai tsokana da faɗa.
Ta ce ita mutum ce mai son cin shinkafa da miya da salad "ya ji nama zuƙu-zuƙu."
A cewarta, abin da ya ba ta tsoro da ba za ta taɓa mantawa ne kuma ya sa ta sheƙa a guje shi ne tsaka.




