Bikin wanka da kashin shanu don girmama wani abin bauta a Indiya
Bikin wanka da kashin shanu don girmama wani abin bauta a Indiya
An wallafa
Ku latsa bidiyon da ke sama don kallon bidiyon:
Ubangijin ƙauyenmu shi ne Beereshwara Swamy, kuma mun yi imanin cewa an haife shi ne a cikin kashin shanu,” in ji Chetan Kumar a lokacin da yake halartar bikin addininsu da suke kira bikin Gorehabba a ƙauyen Gummatapura da ke Indiya.
A kowace shekara, kwana guda bayan bikin Diwali, mutanen ƙauyen Gummatapura kan taru su yi ta shafe jikinsu da kashin shanu bayan sun bi gida-gida sun karɓo shi.
A addinin Hindu dai saniya abar girmamawa ce kuma a wajen wannan biki sun yi imani cewa shafe jiki da kashinta na warkar da cututtuka da dama.
A lokacin annobar cutar korona ma sai da likitoci suka yi ta gargadin ƴan ƙauyen cewa su daina shafa kashin shanun a jikinsu don gudun kaucewa kamuwa da cutar.



