An raba maki tsakanin Chelsea da Man City a Premier League

An wallafa

Chelsea da Manchester City sun tashi 4-4 a wasan mako na 12 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Erling Haaland ne ya fara ci wa City kwallo a minti na 25 a bugun fenariti, sai dai minti biyar tsakani, Chelsea ta farke ta hannun Thiago Silva.

Daga nan Chelsea ta kara na biyu ta hannun Raheem Sterling, sai dai daf da za suje hutu ne City ta farke ta hannun Manuel Akanji.

Bayan da suka yi hutu suna komawa zagaye na biyu ne Erling Haaland ya kara na uku na biyu da ya zura a raga a karawar, Nicolas Jackson ne ya farke wa Chelsea.

Sauran minti hudu a tashi daga wasan, Rodrigo Hernandez ya ci wa City na hutu, bayan da ya buga kwallo ta bugi kafar Silva ta fada raga.

Saura kiris a tashi wasan Chelsea ta samu fenariti, inda Palmer ya buga kwallon ya fada raga.

Da wannan sakamakon City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 28 da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta biyu da kuma Arsenal ta uku.

Wasannin da aka buga a bara tsakanin Chelsea da City:

Premier League Lahadi 21 ga watan Mayun 2023

  • Man City 1 - 0 Chelsea

FA CUP Asabar 8 ga watan Janairun 2023

  • Man City 4 - 0 Chelsea

Premier League Alhamis 5 ga watan Janairun 2023

  • Chelsea 0 - 1 Man City

EFL CUP Laraba 9 ga watan Nuwambar 2022

  • Man City 2 - 0 Chelsea