'Abin da ya sa nake son zama gwamnan Jihar Zamfara'
'Abin da ya sa nake son zama gwamnan Jihar Zamfara'
An wallafa
Dan takarar gwamnan Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya a jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, Ahmad Hashim Tsani, ya ce rashin sanya mutane ciki shirin ci gaban jihar shi ya sa take fuskantar koma-baya a dukkan bangarorin rayuwa.
Ya bayyana haka ne a tattaunawa ta musamman da BBC Hausa.
"Ci gaba mai dorewa ya yi karanci a Jihar Zamfara saboda ba a dauki al'ummomi an sanya su a gaba ba. Duk wani ci gaba da za a kawo ya kamata a ce jama'a ne a gaba," in ji shi.
Ya ce zai mayar da hankali wajen magance matsalolin da suke addabar jihar, kasancewarsa wanda ya yi rayuwarsa gaba daya a cikin jihar.



