Benzema ya ci wa Real kwallo uku rigis a karon farko a bana

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta doke Real Valladolid da cin 6-0 a wasan mako na 27 da suka kara a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.
Minti na 22 da fara tamaula, Rodrygo ya fara cin kwallo, sai Karim Benema ya ci na biyu minti bakwai tsakani, sannan ya kara na uku a minti 32, minti hudu tsakani ya ci na hudu na uku rigis a fafatawar.
Karon farko da tsohon dan wasan tawagar Faransa ya zura kwallo uku rigis a Real Madrid a kakar nan.
Saura minti 17 a tashi wasan Marco Asensio ya ci kwallo, sannan Lucas Vazquez ya kara na shida daf da za a tashi wasan.
Da wannan sakamakon Real ta rage tazarar maki 15 da ke tsakaninta da Barcelona ta dayan teburi, yanzu ya koma 12.
Barcelona tana matakin farko da maki 71, Real Madrid mai maki 59 tana ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya a kakar nan.
Ranar 30 ga watan Disambar 2022, Real ta je ta ci Valladolid 2-0 a La Liga, Karim Benzema ya fara ci mata kwallo a bugun fenariti a minti na 83, sai ya kara na biyu a minti 89.
Wasan farko da Real ta buga tun bayan da aka kammala karawar kasa da kasa da Fifa kan ware don buga manyan wasannin tawagogin duniya.
Wasan da ke gaban Real yanzu shine zuwa Camp Nou ranar Laraba, domin buga karawa ta biyu a daf da karshe a Copa del Rey da Barcelona.









