West Ham ta ɗauki aron Kalvin Phillips daga Manchester City

An wallafa

Dan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips ya ce yana son ƙarawa West Ham ƙarfi a tsakiya, bayan komawarsa ƙungiyar a matsayin aro daga Manchester City zuwa ƙarshen kakar wasanni.

Babu zabin sayar da ɗn wasan mai shekara 28 a yarjejeniyar aron.

Phillips ya sanya hannu kan kwantaragin shekara shida lokacin da ya koma City daga Leeds kan kuɗi fan miliyan 45 a watan Yulin 2022.

“Akwai abubuwan da za a iya cimmawa a wannan bangaren na biyu kakar wasanni. Kuma ina son zama ɗaya daga ciki” a cewarsa.

“Na shigo zan tarar da matasan ‘yan kwallo da za mu iya fafatawa daga nan zuwa ƙarshen kakar wasanni, mu sanya magoya bayan West Ham farin ciki zuwa ƙarshen kaka.”

Phillips ya fara buga wasa ne sau biyu kacal cikin watanni 18 da ya kwashe a City, ya kuma buga wasanni Premier 16, inda yake neman hannu a ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta.

Kungiyoyi da dama ciki har da Newcastle da Crystal Palace da kuma Juventus suna nuna son ɗaukar ɗan wasan.

Wannan aro da Hammers ta samu zai iya ƙara ƙwarin tsakiyarta, bayan da kocinta David Moyes ke fama da masu jinya da dama.

Lucas Paqueta da Michail Antonio na jinya ta tsawon lokaci, yayin da ɗan wasan tsakiyar Mexico Edson Alvarez bai buga wasan FA ba da Bristol City sakamakon rauni.

West Ham da ke matsayi na shida a Premier ta kai matsayi sili ɗaya kwale a Europa wanda za a ci gaba da bugawa a watan Maris.