Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaban Afirka ta Kudu na fuskantar tsigewa
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu na fuskantar tsigewa bisa abin da wani kwamiti bincike a kasar ya gano cewa "mai yiyuwa" ya sabawa dokar kundin tsarin mulki a kan yadda ya tafiyar da batun wata sata a gonarsa.
Al’amarin ya ja hankalin jama’a ne a watan Yuni lokacin da tsohon jami’in leken asiri na Afirka ta Kudu, Arthur Fraser, ya zargi shugaban kasar da boye kudaden da aka sace na dala miliyan 4 a gonarsa.
Kudin da aka boye a cikin katifa a gonarsa ya sa jam'iyyun hammaya sun rika zarginsa da halata kudin haram.
Sai dai Shugaban na Afirka ta Kudu ya musanta aikata wani abu da ya saba wa doka.
Rahoton na kwamitin da ya kunshi alkalai ya sa Shugaba Cyril Rampphosa ciikin wani yanayi na tsaka mai wuya wanda sa yaki da cin hancin da rashawa a abubuwan da zai fi ba fifiko a lokacin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa.
Sai dai duk da cewa bai zama dole a yi amfani da shawarwarin da kwamitin ya bayar ba amma jam'iyyun hammaya za su iya amfani da rahoton wajen yin kira da a kara gudanar da bincike mai zurfi a kan zarge-zargen.
Kuma idan an same shi da laifi toh watakila wannan zai sa a tsige shi daga mukaminsa na shugaban kasa.
Rahoton wanda ya kushi manyan kundi guda uku ya sa ana tambayoyi a kan dalilin da ya sa Mr Raamophosa ya ajiye makudan kudade a gonarsa.
Da kuma dalilin da ya sa ya rika jinkirin zuwa caji ofis din 'yan sanda domin ya shigar da kara sannan kuma ana zarginsa da yin rufa-rufa
Haka kuma kwamitin ya ce akwai alamar tambya game da bayanin da shugaban ya yi a kan cewa miliyoyin sun fito ne daga baunar da ya sayar wadda yake kiwo.
Sai dai kwamitin ya yi amannar cewa akwai tambayoyi da dama da ba a amsa ba kuma ya bayyana zarge-zargen da ake ta yi wa shugaban a matsayin al'amari mai matukar muhimamci.
Sai dai a martamin da ta mayar jam'iyyar ANC mai mulki ta kira wani taro da manyan jiga-jigan kungiyar a ranar alhamis.
Duk da cewa ba a bayyana abubuwan da taron zai tattauna ba amma ana kyautata zaton rahoton na cikin abubuwan da taron nasu zai mayar da hankali a kai.
A daya bangaren kuma ofishin shugaba kasa ya ce Mr Ramophosa na nazari a kan shawarwarin da kwamitin ya bayar kuma nan bada jimawa ba zai mayar da martini.