An yi sauyi da yawa a jadawalin Man United a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Mahukuntan Premier League sun yi gyara a jadawalin wasan da ya kamata Manchester United ta kara da Brighton da na West Ham United.
Tun farko an tsara cewar Erik ten Hag zai fuskanci Roberto De Zerbi a Premier League ranar 19 ga watan Maris.
Kungiyoyin biyu kowacce ta ci kwata fainal a makon jiya a FA Cup, za kuma su fuskanci juna a Wembley a daf da karshe ranar 8 ga watan Afirilu.
Kenan United za ta ziyarci Brighton a Amex ranar Alhamis 4 ga watan Mayu a Premier League, Brighton ce ta fara cin United 2-1 da fara kakar bana ranar 7 ga watan Agusta a Old Trafford.
Haka kuma wasan da ya kamata United ta buga da West Ham ranar Asabar 6 ga watan Mayu, yanzu za su kece raini ranar Lahadi 7 ga watan Mayu.
Gumurzun da United ya kamata ta karbi bakuncin Chelsea ranar Asabar 22 ga watan Afirilu an dage wasan, sakamakon fafatawar da za ta buga da Sevilla a Europa League.
United za ta karbi bakuncin Sevilla ranar 20 ga watan Afirilu a wasan farko a quarter finals, sannan ta ziyarci Sifaniya ranar 20 ga watan Afirilu.
Saboda haka za a sanar da sabuwar ranar da Chelsea da United za su buga a tsakaninsu a Premier League.
Haka kuma karawar da United za ta yi da Wolverhampton a Old Trafford da wanda za ta ziyarci Bournemouth ba a fayyace ranar buga wasannin ba.
Amma wasan da United za ta yi da Fulham na karshe a bana a Premier League yana nan kamar yadda aka tsara, ranar 28 ga watan Mayu a Old Trafford.
United wadda ta lashe Carabao Cup a bana na farko tun bayan 2016/17 karkashin Jose Mourinho tana ta uku a teburin Premier League.











