Me ya sa mashigar Rafah a Gaza ke da muhimmanci
Me ya sa mashigar Rafah a Gaza ke da muhimmanci
An wallafa
Falasdinawa na taruwa a kan iyakar Rafah, wadda ake tsallakawa zuwa cikin Masar a kudancin Zirin Gaza da fatan barin yankin kafin wani hari ta kasa da ake tsammanin Isra'ila za ta kai.
Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa za a bude mashigar ga mutanen da ke da shaidar zaman 'yan kasa biyu su fice daga Zirin, sannan a bai wa kayan bukatun jin kai damar shiga, ba tare da bayar da lokaci ba.



